IQNA

An Kame Mutumin Da Ke Aikewa Musulmi Da Wasiku Yana Musu  Barazana

23:54 - June 13, 2018
Lambar Labari: 3482754
Bangaren kasa da kasa, an kame wani mutum dan shekaru 35 da yake aikewa da wasiku yana yi musulmi barazana a kasar Birtaniya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na bbc bangaren turanci ya habarta cewa, an kame wani mutum dan shekaru talatin da biyar da yake aikewa da wasiku yana yi musulmi barazana a kasar Birtaniya da yake zaune a raewacin kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan mutum yana daga cikin mutanen da ske nuna tsananin kiyayya ga musulmi a kasar ta Birtaniya.

A cikin wasikun da yake aikewa, yana yin barazana ga musulmi, tare da tsorata su, da kuma yi musu barazana.

Tun bayan kai hare-haren ta’addancin da aka yi a  lokutan bayan-bayan nan akasar Birtaniya, kyamar musulmi na ci gaba da karuwa a sassa daban-daban na kasar.

3722631

 

 

 

 

 

 

captcha